- Wannan wata qasida ce game da Yusufu Annabi ne. Don neman karin bayani game da jerin shirye-shiryen TV masu suna iri ɗaya, A duba Yusuf Annabi (Wasu adadin shirye-shiryen talabijin).
Yusuf (Larabci: النبي يوسف (ع)) yana daga cikin Annabawan Bani Isra'il kuma ɗa ne ga Annabi Yaƙubu, bayan kasancewarsa Annabin Allah, ya mulki ƙasar Misra tsawon shekaru, cikin Alkur'ani akwai sura guda ɗauke da sunan Yusuf wace cikinta an kawo labarin filla-filla.
Lokacin da Yusuf yake yaro ƴan uwansa sun jefa shi cikin rijiya; sai dai wasu jama'a suka cece shi daga cikin rijiya suka fito da shi, suka tafi da shi a matsayin bawa sannan suka sayar da shi ga Sarkin Misra, Zulaikha Matar Sarkin Misra ta ɗimauta da kyawun da Yusuf yake da shi, sai dai cewa bayan Yusuf ya ƙi yarda ya mika wuya ga buƙatarta, sai ta tuhume shi da ha'inar Sarkin Misra ta sa a ka jefa shi cikin kurkuku.
Bayan shuɗewar shekaru Yusuf ya tabbatar da kasancewarsa bai aikata lefi ba, an sako shi daga kurkuku saboda ya ba da fassarar mafarkin da Sarki ya yi, da kuma kawo mafita dangane da barazanar da Misra take fuskanta daga fari da rashin ruwan sama, Yusuf ya samu farin jini da karɓuwa wurin Sarkin Misra wanda daga ƙarshe ya naɗa shi matsayin wazirinsa.
ƙissar da ta zo cikin Alkur'ani dangane da Yusuf tasha bamban da wacce take cikin littafin At-Taura; daga jumlarta kan asasin Alkur'ani, ƴan'uwan Yusuf wanda suke uba ɗaya da su sune suka nemi Yaƙubu ya yarda su tafi Sahara tare da Yusuf, amma kan asasin At-Taura ya zo cewa Yaƙubu da kansa ya nemi Yusuf ya bi ƴan'uwansa su fita tare.
Yusuf ya yi shekaru 120 a duniya kuma an binne shi a ƙasar Palasɗinu.
![]() Kabarin da ake dangantawa da Yusuf (A.S) da yake a Falasɗinu | |
Suna a cikin Kur'ani | Yusuf |
---|---|
Maimaitauwar sunan a Kur'ani | Sunan Annabi Yusuf (A.S) ya zo sau 27 a cikin ayoyi 26 na Al-kur'ani a cikin surori kamar haka: Yusuf. An'am. Gafir |
Sunan a cikin littafi Mai tsarki | Joseph |
Laƙabi | Azizu Misra |
Tsawon rayuwa | Shekaru 120 |
Mahallin rayuwa | Falasɗinu |
Iyaye | Sayyidina Yaƙub, Rahila |
Nasaba | Daga zuriyar Ibrahim (A.S) |
Mata | Zulaikha bisa wata magana |
Ƴaƴa | Ifrim (Kakan Yusha'u Bin Nun) |
Mutanensa | Banu Isra'il |
Aiko shi | an aiko shi Annabi yana da shekara 11 |
Bayan | Annabi Yaƙub |
Littafi | Bibaraz bin Lawi shi ne ya kasance Halifan Yusuf |
Annabawa da suka yi zamani tare da shi | Addinin Hanif (Kaɗaita Allah) |
Yaƙoƙi | Suratul Yusuf. jefa shi cikin rijiya. rayuwa a gidan Azizu Misra. Tarkul Aula da Yusuf ya aikata |
Faɗaɗuwar Saƙo | Labarin fari na shekaru bakwai a Misra da kuma hijirar Bani Isra'ila zuwa Misra da na samu: |
Masu Adawa | Banu Isra'il |

Matsayi
Yusuf ɗa ne ga Yaƙub, wanda ya kasance daga Annabawan Banu Isra'il sunan mahaifiyarsa Rahil,[1] ya kasance yana da ƴan'uwa goma sha ɗaya tsakaninsu Binyaminu ne kaɗai suke uwa ɗaya da shi,[2] Yusuf shi ne ƙaramin cikinsu in banda Binyaminu wanda shi kaɗai ne ƙaninsa.[3] Sunan Yusuf ya zo karo 27 a cikin Alkur'ani,[4] sura ta goma sha biyu cikin Alkur'ani ta zo da sunansa, Alkur'ani ya bayyana Yusuf daga cikin muklisan bayin Allah,[5] a cewar Allama Ɗabaɗaba'i, bawai kaɗai Yusuf yaki miƙa wuya ga buƙatar Zulaikha ba, bari dai hatta cikin zuciyarsa bai karkata zuwa ga abin da take so ba,[6] haka kuma cikin Alkur'ani an ƙidaya shi cikin masu kyautata aiki.[7]
Annabta
Yusuf yana daga cikin manya-manyan Annabawa,[8] cikin wata riwaya daga Imam Baƙir (A.S) tare da jingina da ayoyin Alkur'ani an bayyana Yusuf matsayin Annabi kuma Manzo,[9] bisa abin da ya zo cikin tafsirin Amsal, mafarkin Yusuf wanda cikinsa ya ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna yi masa sujjada, ƙari kan bada labarin samun mulki da dukiya wannan mafarki yana bayanin Annabtarsa a nan gaba,[10] Allama Ɗabaɗaba'i yana ganin wannan mafarki matsayin ɗaya daga cikin misdaƙan Annabtar Yusuf wanda ya zo cikin aya ta 6 suratul Yusuf, da yake nuna samun muƙamun Annabta.[11]
wasu adadin malaman tafsiri na shi'a da ahlus-sunna a wutsiyar aya ta 15 suratul yusuf suna cewa a lokacin da Annabi Yusuf (A.S) yake cikin rijiya ne Allah ya ba shi annabta tare da yi masa wahayi.[12] Ƙazi Nurullahi Shushtari ya ce a wannan lokaci Yusuf ya kasance ɗan shekara goma sha ɗaya a duniya.[13] a cewar Ɗuraifi daga malaman tafsiri na ahlus-sunna, an baiwa Yusuf annabta tun kafin balagarsa.[14]
Tarihin Rayuwa
Cikin Alkur'ani a suratul Yusuf an yi bayanin ƙissar rayuwar Yusuf filla-filla, Alkur'an ya kira wannan ƙissa da sunan mafi kyawun ƙissoshi,[15] ciki an yi bayani rayuwarsa tun yana yaro ƙarami da kuma yanda aka jefa shi cikin rijiya, sai da shi ga Sarkin Misra, ƙissar Zulaikha da Yusuf, jefa cikin Kurkuku da haɗuwarsa da Mahaifinsa da ƴan uwansa a ƙasar Misra.[16]
Wurga Shi Cikin Rijiya Da Kai Shi Misra
- Ku duba: Suratul Yusuf
Labarin rayuwar Yusuf da ta zo a Alkur'ani cikin suratul Yusuf bayaninta ya zo filla-filla a wannan sura, kan asasin Alkur'ani ya gayawa mahaifinsa mafarkin da ya gani na Rana da Wata da Taurari goma sha ɗaya suna yi masa sujjada, sai mahaifinsa ya ce masa kada ya sake ya gayawa ƴan'uwansa wannan mafarki, saboda idan ya gaya musu za su shirya masa makirci mai hatsari su kashe shi.[17] Malaman tafsiri sun fassara Taurari goma sha ɗaya da ƴan'uwan Yusuf, sannan abin nufi daga Rana da Wata su ne mahaifinsa da mahaifiyarsa, bayan Yusuf ya samu ɗaukaka duniya da lahira sai suka faɗi suna girmama shi.[18]
Ƴaƴan Annabi Yaƙubu (A.S) sun kasance suna cewa lallai Yusuf ya fi samunn soyayya a wurin Ubanmu.[19] wata rana sai suka roƙi Yaƙubu ya basu izini su su fita wasa tare da Yusuf su je sahara, kuma suka yi alƙawari za su kula da shi,[20] bayan sun fita sahara sai suka wurga Yusuf cikin rijiya, suka dawo gida suka cewa Yaƙubu Kura ta cinye shi,[21] kamar yanda ya zo a Alkur'ani Yaƙubu bai yarda da maganarsu ba,[22] bayan wani lokaci sakamakon raɗaɗi da tsananin da kuma yawan kuka kan Yusuf sai ya makance,[23] an tambayi Imam Sadiƙ (A.S): zuwa wanne haddi Yaƙubu ya yi baƙin ciki kan Yusuf ? sai ya ce: gwargwadon baƙin cikin mata saba'in da ƴaƴan da suka haifa suka mutu,[24] wasu Ayarin matafiya sune suka fitar da Yusuf daga cikin wannan rijiya, suka tafi da shi Misra matsayin bawa, sai babban wazirin Misra ya saye shi ya kai shi gidansa.[25]
Kyawun Yusuf Da Labarin Zulaikha
Cikin litattafan ƙissoshin Alkur'ani an siffanta Yusuf matsayin kyakkyawan Namiji,[26] [Tsokaci 1] da wannan dalili ne Zulaikha matar Sarkin Misra ta fitinu da shi, ta kai ta neme shi da aikata alfasha sai dai cewa Yusuf ya yi tsantseni tare da ganin dalilin Ubangijinsa wanda aka bayyana shi wani abu ne daga jinsin ilimi da yaƙini da ya keɓantu da ma'abota iklasi,[27] bai miƙa wuya ga buƙatar Zulaikha ba.[28] [Tsokaci 2] Sai dai kuma wannan labari ya je kunnen mutanen gari, wasu gungu daga matan cikin gari suka tuhumi Zulaikha, sai Zulaikha ta shirya zama tare da gayyatar mata guda arba'in[29] daga matan hakimai ta sa aka kawo musu kayan marmari na lambu daga lemon zaki, [30] aka basu sannan ta umarci Yusuf ya shigo wannan majlisi da ta shirya, lokacin da ya shigo majalisin, sai waɗannan mata suka gigice da ganin kyawunsa suka yi iƙrari da kyawunsa, suka yayyanka yatsun hannunsu saboda ɗimauta da kyawunsa.[31]
Tarjama: Rashin hankali na mai hauka, masu hankali ne suka san shi Ba ya iya jurewa rashin hakuri Idan ka ga shi kuma ka daina gane 'ya'yan itace na tuffa Zai halatta ka zargi Zulaikha. .[32]
Bayan wannan zama, sai ya zama ko wace rana suna nemansa da alfasha, sai ya roƙi Ubangiji ya ƙaddara kai shi Kurkuku domin ya kuɓuta daga gare su, bayan wasu ƴan kwanaki sai Zulaikha ta ba da umarni a kai shi Kurkuku.[33][Tsokaci 3]
Fassarar Mafarkin Sarkin Misra Da Aziz Misra
Sakamakon sanin fassarar Mafarki, ya fassara mafarkin abokan zaman gidan Kurkuku su biyu ɗaya daga cikinsu za a kashe shi, ɗaya kuma za a sake shi zai kuma samu matsayi a wurin Sarkin Misra,[34] bayan wasu shekaru da wannan labari sai Sarkin Misra ya yi mafarki ya ga ramammun Shanu guda bakwai suna cinye ƙosassu guda bakwa, haka kuma ya ga korayen zangarniya guda bakwai da kuma wasu busassu guda bakwai,[35] sakamakon gazawar masu fassara mafarkin Sarkin kan wannan mafarki da ya yi, kwatsam sai wannan wanda ya zauna tare da Yusuf a Kurkuku ya tuna da Yusuf, ya ce Yusuf zai iya fassara wannan mafarki mai bada damuwa da tsoro.[36]
Sai ya tafi kurkuku ya tambayi Yusuf fassarar wannan mafarki, Yusuf ya ce: za ku samu shekaru bakwai masu albarka da yawan ruwa, bayansu kuma za ku fuskanci shekaru bakwai masu tsanani da fari, sai Yusuf ya basu shawara domin samun kuɓuta daga fari shekara ta farko su yawaita shuka da noma, sannan sauran amfani gona da ya rage daga wanda suka ci su barshi a zangarniyarsa su ajiye shi a ma'ajiya don ya wanzu lafiya ba tare da lalacewa ba.[37]
Sakamako Yusuf ya fassara mafarkin Sarki sai ya karɓi shawarar da Yusuf ya bayar game da magance fari, sannan ya nemi a kirawo masa Yusuf, sai dai cewa Yusuf ya gaya wanda Sarki ya aiko wurinsa cewa ya tambayi Sarki kan matan da suka yayyanke hannuwansu da kuma game da kai shi Kurkuku, sai Sarki ya yi bincike game da wannan maudu'i, ya sa aka kira waɗannan mata. Matan Misra suka bada shaida kan rashin laifin Yusuf, ita ma Zulaikha ta yi iƙrari kan abin da ta aikata.[38] Bayan fassarar mafarki da tabbatar rashin lefin Yusuf, sai Sarki ya sa aka sake shi ya fito daga kurkuku, sannan kuma ya naɗa shi wazirinsa kuma Aziz Misra.[39]
Haɗuwar Yusuf Da Danginsa
Ayatullah Jawadi Amoli:
Wasu suna da zikirin Yunusa ﴿ لا إِلهَ إِلّ انتَ سْحانَكَ إِنِي كونتو من آلَّعليمينَ﴾... wasu ba'ari suna da zikirin Yusuf; Kasancewar Yusuf mai albarka, a cikin dukkan hatsarin zamaninsa, ya yi hakuri lokacin da aka jefa shi cikin rijiyar. Ya yi hakuri lokacin da aka daure shi. Da ya kai ga mulki da daraja da sarauta sai ya ce: ‚ ya Ubangiji ka bani mulki ka sanar dani fassarar daga fassarar labarai... ka karbi raina matsayina na musulmi; , a yanayin hadari da rashin lafiya, neman mutuwa ba fasaha ba ne; Amma idan ya ce da dukkan karfinsa, Ya Allah ka karbi raina, abin ya kawo sauyi... Masu ambaton Yusufu suna rokon Allah da kyakykyawan karshe, kyakykyawan karshe da kyakykyawan karshe na daga cikin mafificiyar falala.
Kulaini, Al-Kafi, bugun shekara ta 1407 h, ƙ, juzu'i 6 shafi na 391, Ibn Qaulawaihi, Kamilul Al-ziyarat, shekarar 1356 h, shamsi, shafi na 106
Lokacin da Misra take fuskantar fari da yankewar ruwa, shi ma garin Kan'an ya fuskanci wannan matsalar, da wannan dalili ne Yaƙubu ya tura ƴaƴansa ƙasar Misra domin samo Alkama,[40] Yusuf da ya ga ƴan uwansa take ya gane su, sai dai cewa su ba su gane shi ba.[41] ya kyautata mu'amala da su[42] tare da aika rigarsa zuwa ga Yaƙubu sai ya warke daga makanta idonsa ya buɗe ya dawo yana gani,[43] bayan nan sai Yaƙubu tare da ƴaƴansa suka tafi Misra domin ganin Yusuf.[44]
Aure Da Ƴaƴa
bisa naƙalin Mas'udi marubucin tarihi a ƙarni na huɗu h ƙamari, Yusuf ya yi aure a Misra kuma ya haifi ƴaƴa biyu da sunan Ifra'im (Kakan Yusha'u Bin Nun) da Misha.[45]
Aurensa Da Zulaikha
Cikin ba'arin wasu riwayoyi Magana ta zo dangane da aure Yusuf tare da Zulaikha bayan ya samu muƙamun Aziz Misra, alal misali ya zo cikin wani hadisi cewa Yusuf ya ga wata mata na cewa godiya ta tabbata ga Allah wanda ya mayar da bawa Sarki sakamakon ɗa'arsa, kuma ya mayar da Sarki bawa sakamakon saɓonsa, sai ya tambayeta wacece ke sai tace ni ce Zulaikha, sai Yusufu ya aureta,[46] hatta ba'arin wasu riwayoyi sun kawo Magana cewa Zulaikha ta koma matashiya albarkacin addu'ar Yusuf, bayan ta canja sai ya aureta,[47] sai dai cewa wasu masu bincike kan waɗannan riwayoyi sun bayyana cewa cikin sanadinsu da abin da yake cikinsu akwai matsala da rauni, suna ganinsu matsayin riwayoyi da ba za a iya dogara da su ba,[48] cikin ba'arin wasu naƙali ya zo cewa dukkanin ƴaƴan Yusuf guda biyu Zulaikha ce ta haifa masa su.[49] Kan asasin aya ta 42 suratul Yusuf, lokacin da Yusuf yake a kurkuku, ya faɗawa ɗaya daga abokansa zamansa a kurkuku za a sake shi, ya ce masa idan ka fita ka tunatar da Sarki batuna, sai dai cewa Shaiɗan ya mantar da shi tunatar da Sarki, da wannan dalili Yusuf ya zauna a kurkuku tsawon shekaru, a wannan batu akwai saɓanin ra'ayoyi tsakanin Malaman tafsir, wasu ba'arinsu sun ce abin ake nufi shi ne Shaiɗan ya mantar da Yusuf Ubangijinsa, wasu kuma sun ce Shaiɗan ya zama sababin mantuwar abokin zamansa a kurkuku wanda aka saka dagaya gayawa Sarki cewa Yusuf bai da lefi, Allama ɗabaɗaba'i yana ganin Magana ta farko bata dacewa da bayanin da Alkur'ani ya zo da shi ƙarara, saboda Alkur'ani ya ƙidaya Yusuf daga Bayinsa masu Iklasi, [yadash ][50] Malaman Tafsiri suna ganin abin da Yusuf ya aikata ya kasance daga Tarkul Aula (bari abin da ya fi dacewa) saboda su Annabawa suna kan ƙololuwar martabar tauhidi wannan miƙdari na kamun kafa da sabubban duniya ba ya dacewa da muƙaminsu.[51]
Tarkul Aula
- Ku duba: Tarkul Aula
Kan asasin aya ta 42 suratul yusuf, yayin da Yusuf yake kurku ya sami labarin sakin ɗaya daga cikin fursunoni da suke zaune tare, kafin ya fita sai ya ce masa idan ka fita ka je wurin sarki ka tunatar da shi cewa an ɗaure ni ba tare da na aikata lefi ba, sai dai kuma shaiɗan ya mantar da shi, da wannan dalili ne Yusuf ya ci gaba da zama a fursun tsawon shekaru. game da wannan batu malaman tafsiri suna da saɓanin fahimta. wasu ba'ari sun ce shaiɗan ya mantar da Yusuf tunawa da Allah da Allah, a ra'ayin wasu kuma sun tafi kan cewa shaiɗan ya zama sababin wannan fursuna da aka saka ya fito daga fursun ya manta ya isar da sakon Yusuf wurin Sarki. Allama Ɗabaɗaba'i yana ganin cewa ra'ayi na farko ya yi hannun riga da abin da kur'ani ya kawo karara; saboda kur'ani da kansa ya bayyana cewa Yusuf yana daga tsarkakakkun bayin Allah da Allah ya tsarkake su daga aikata duk wani zunubi.[Tsokaci 4]a wata majiyar ya zo cewa babu sanda Shaiɗan zai iya tasiri ya kutsa cikin kwakwalen katangaggun bayin Allah.[Tsokaci 5] [52] ta ko wace fuska malaman tafsiri suna ganin abin da Yusuf ya yi ba komai bane face tarkul aula (Rashin aikata abin da ya fi kamata da shi), saboda Annabawa da mutanen da suke da babban mukami cikin kadaita Allah baya dacewa da mukaminsu da sha'aninsu kamun kafa da wannan mikdari daga sabubban rayuwar duniya.[53] A cikin wasu hadisan Tarkul aula, an danganta wasu tarkul aula (barin abin da ya fi kamata) ga Yusuf.[54] Kamar yadda wadannan hadisai suka nuna, lokacin da Annabi Yakub ya zo wurin Yusuf bayan rabuwa tsawon shekaru, Yusuf kasancewarsa matsayinsa sarki, bai bar gadon sarautarsa ya sauko kasa ba don girmama mahaifinsa da ya tsufa.[55] da wannan dalili ne ma aka cire annabta daga tatson Yusuf[56] aka mayar da ita cikin tsatson Lawi dan uwan Yusuf.[57] Jafar Sobhani, daya daga cikin malaman tafsirin Shi'a yana ganin cewa wadannan hadisan ba su dace da abin da ya zo a Alkur'ani ba; Domin kuwa kamar yadda ayoyin Alqur'ani suka nuna Hazrat Yusuf ya girmama mahaifinsa sosai.[58] Muhammad Sadiƙ Tehrani, marubucin Tafsirin Furƙan, ya yi imanin cewa wadannan hadisai daga Isra'ila'liyyat (Tatsuniyoyin yahudawa) suke, kuma suna da matsaloli ta hanyoyi daban-daban.[59]
Bambanci Tsakanin Labarin Yusuf A Cikin Kur'ani Da Attaura
Kan asasin abin da Allama Ɗabaɗaba'iya nakalto daga Attaura sabanin Kur'ani,[60] ya zo cewa Annabi Yusuf (A.S) ya yi mafarki ya ga taurari da rana da wata suna masa sujjada, sai ya labartawa `yan uwansa, hakan ne ya zama sanadiyya suka fara yi masa hassada, suka shida matukar damuwa sakamakon suna jin tsoro cewa nan gaba zai zama shugabansu ya daukaka sama da su. Haka nan, bisa abin da ya zo a Attaura, a lokacin da ya bayyana wa babansa Yakub mafarkin, sai Yakub ya fusata da shi, ya ce: “Shin ni da mahaifiyarka da `yan’uwanka goma sha daya ne muka yi maka sujjada?![61] wani bambanci na daban kan asasin rahotannin kur'ani, `yan uwan Yusuf sun bukaci taimakon Yakub ya ba su Yusuf su fita su je sahara,[62] amma cikin rahotan Yakub ne da kansa ya nemi Yusuf ya raka `yan uwansa domin su je su ga cewa dabbobinsu suna nan lafiya?.[63]
Wafati Da Mahallin Da Aka Binne Shi
A cewar Mas'udi marubucin tarihin musulmai a ƙarni na huɗu h ƙamari, haƙiƙa Yusuf ya rayu shekara 120, lokacin da zai mutu Ubangiji ya yi masa wahayi da ya bada haske da hikimar da yake hannunsa zuwa ga Bibarazu Bin Lawi Bin Yaƙub, sai ya Yusuf ya kira Alu Yaƙubu waɗanda a wannan lokaci sun kai adadin mazaje 70 ya gaya musu cewa ba da daɗewa wasu jama'a za su yi galaba a kanku , zaku shiga azaba mai tsanani, har zuwa lokacin da Ubangiji zai taimake ku ta hannun ɗaya daga ƴaƴan Lawi wanda ake kira da suna Musa,[64] bayan wafatin Yusuf wasu jama'a sun nemi binne shi a unguwarsu, domin gudun rigima sai aka binne shi a Misra cikin wata Akwatun Marmara, aka binne shi a Nil, bayan shuɗewar shekaru sai Musa ya ciro jana'izarsa daga wannan wuri[65] a cewar Yaƙutul Hamawi marubucin tarihi a ƙarni na shida da bakwai an binne Yusuf ne ƙasar Palasɗinu.[66]
Yusuf Cikin Ayyuka Fasaha
- Asalin Maƙala: ƙissar Annabi Yusuf (wasu adadin shirye-shiryen Talabijin)
Labarin Yusuf ya bayyana a cikin ayyukan fasaha da watsa labarai kamar zane-zane, aikin tayal, adabi, sinima da talabijin.[67]A shekara ta 2007, an watsa shirye-shiryen talabijin na Annabi Yusuf (A.S) a gidan talabijin na Iran. Baiti waƙar da zai zo a ƙasa shi ne na Hafez Shirazi, mawaƙi a ƙarni na 8, inda aka ambaci labarin Yusuf.
Bayanin kula
- ↑ Safi, ؐƙissahaye ƙur'ani, 1379, shafi na 106.
- ↑ Safi, ؐƙissahaye ƙur'ani, 1379, shafi na 106.
- ↑ Safi, ؐƙissahaye ƙur'ani, 1379, shafi na 87.
- ↑ Jafari, “Namhaye Payambaran dar Kur’an” shafi na 25-26.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 24.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 Hijira, juzu'i na 11, shafi na 130.
- ↑ Suratul An'am, aya ta 84.
- ↑ Jazayeri, Al-Nurul Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 259.
- ↑ ƙutbuddin Ravandi, ƙasas Al-Anbiya, 1430 AH, shafi na 348.
- ↑ Misali, duba Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 9, shafi na 310.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 11, shafi na 82.
- ↑ Misali, duba: Sheikh Tusi, al-Tibyan, juzu'i na 6, shafi na 109; Qortubi, Al-Jamae Ahkam al-Qur’an, 1384 A.H., juzu’i na 16, shafi na 56; Muhammad bin Abd al-Wahhab, Tafsirul Ayat Alkur’ani, Jama’atul Imam Muhammad bin Saud, juzu’i na 5, shafi na 132.
- ↑ Shushtri, Al-Sawarim al-Muhriqa, 1367, shafi na 312.
- ↑ Al-Tarifi, al-Tafsir al-Walbayan li Ahkam al-Qur’an, 1438 AH, juzu’i na 3, shafi na 1617.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 3.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 8 zuwa ta 100.
- ↑ Suratul Yusuf aya ta 4 da ta 5.
- ↑ Ibn Kathir, ƙasas Al-Anbiya, 1416 Hijira/1996 Miladiyya, shafi na 191.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 8.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 12.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 17.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 84.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 242.
- ↑ Suratul Yusuf aya ta 10 da ta 19.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 21.
- ↑ Misali duba: Tabataba'i, Al-Mizan, 1391H, juzu'i na 11, shafi na 122. Jazayeri,Al-nurul Al-Mubin, 1423 AH, shafi na 217; Balaghi, ƙasas Kur'an, 1380, shafi na 98; Safi, ƙissahaye ƙur'an, 1379, shafi na 114 da 115.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1391 AH, juzu'i na 11, shafi na 129.
- ↑ Safi, ƙissahaye Kur'an, 1379, shafi na 115 da 116; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 23.
- ↑ Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 396.
- ↑ Ɗabarasi, Majma Al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 396.
- ↑ Safi, ƙissahaye Kur'an, 1379, shafi na 117 da 118; Duba kuma Suratul Yusuf, aya ta 30 da ta 31.
- ↑ Sheikh Jazayeri ya rubuta littafin "Al-Nur al-Mubin," wanda aka wallafa a shekara ta 1423 hijira. A shafi na 221, littafin ya yi magana akan labarin Annabi Yusuf (A.S) da Zulaikha, wanda ya bayyana a cikin Suratul Yusuf, ayoyi 33 zuwa 35.
- ↑ Jazayeri, Al-Nur Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 221; Duba kuma suratu Yusuf, aya ta 33-35.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'an, shafi na 105-106; Ka duba suratu Yusuf aya ta 41.
- ↑ Jazayeri, Al-Nur Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 223; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 43.
- ↑ Jazayeri, Al-Mur Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 223; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 44 da ta 45.
- ↑ Jazayeri, Al-Nur Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 223; Duba kuma suratu Yusuf, aya ta 47-49.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'an, shafi na 105-106; Ka duba suratu Yusuf aya ta 50 da ta 51.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'an, shafi na 108.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'an, shafi na 110.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'ani, shafi na 109; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 58.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'ani, shafi na 110; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 59.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'ani, shafi na 119; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 93-96.
- ↑ Balaghi, ƙasas Kur'ani, shafi na 119; Duba kuma Suratul Yusuf aya ta 100
- ↑ Masoudi, Isbatul Al-Wasiyya, 2004, shafi na 49.
- ↑ ƙutbuddin Ravandi, ƙasas Al-Anbiya, 1430 AH, shafi na 351.
- ↑ Jazayeri, Al-Nurul Al-Mobin, 1423 AH, shafi na 234.
- ↑ Duba: Ma’arif wa Digaran, “Barasi riwayat tafsiri Fariƙaini dar Mas'aleh Izdiwaj Hazrat Yusuf Ba Zulaikha”, shafi na 7-32.
- ↑ مقدسی، البدء و التاریخ، بور سعید، ج۳، ص۶۹؛ ابن کثیر، البدایة و النهایة، ۱۴۰۷ق، ج۱، ص۲۱۰؛https://pasokh.org/fa/Question/View/73787/آیا-از-فرزندان-و-نوادگان-حضرت-یوسف-ـ-علیه-السلام-ـ-پیامبر-هم-شد-و-اصلاً-یوسف-ـ-علیه-السلام-ـ-فرزند-داشته-است
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 11, shafi na 181
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 9, shafi na 414.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 11, shafi 181
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 9, shafi na 414.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 70, shafi na 223.
- ↑ Faizul Kashani, Al-Wafi, 1406 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 873.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 312; Sheikh Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 252.
- ↑ Qommi, Tafsirul Qommi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 356.
- ↑ Sobhani, Manshur Javid, 1433 AH, juzu'i na 11, shafi.472.
- ↑ Sadeghi Tehrani, Al-Furqan fi Tafsirin Qur'an, 1365, juzu'i na 15, shafi na 208.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 4.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 11, 261.
- ↑ Suratul Yusuf, aya ta 12.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 11, shafi na 261.
- ↑ Masoudi, Isbatul Al-Wasiyya, 2004, shafi na 74.
- ↑ Masoudi, Isbatul Al-Wasiyya, 2004, shafi na 75.
- ↑ Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 1, shafi na 478.
- ↑ <a class="external text" href="http://vista.ir/article/351963">«چهار سال با یوسف پیامبر»</a>
Tsokaci
- ↑ hakika Yusuf ya kasance kyakkyawan namiji mai zurfin hankali da tunani. Sarauniyar yarinya ce kyakkyawa, kuma ita ce uwargidan sarakuna da manyan mutane. Libra, Ismailian Publications, juzu'i na 11, shafi na 126.
- ↑ Allama Tabataba'i a cikin tafsirul Al-mizan ya jaddada cewa gidan sarakuna da mashahuran al'umma na da tsare-tsare iri-iri da ababen more rayuwa don cimma burinsu da manufofinsu sannan kuma gidan Aziz Masar ya kasance kamar haka ne ya kamata ya rudi Yusuf ya kai shi ga aikata zunubi. . Tabatabai, Al-Mizan, 1391 AH, juzu'i na 11, shafi na 122.
- ↑ Allameh Tabatabai ya jaddada a cikin Al-mizan cewa gidan sarakuna da mashahuran al'umma na da tsare-tsare iri-iri da kayan aiki don cimma burinsu da manufofinsu sannan kuma gidan Aziz Masar ya kasance kamar haka ne don kama Yusuf ya kai shi ga aikata zunubi.
- ↑ Suratul Yusuf aya ta 24:إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُخْلَصِینَ. lallai shi yana cikin katangaggun bayinmu
- ↑ Suratul Hijri aya ta 39-40...لَأُزَیِّنَنَّ لَهُمْ فِی الْأَرْضِ وَلَأُغْوِیَنَّهُمْ أَجْمَعِینَ* إِلَّا عِبَادَکَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِینَ. zan kayata musu zunubansu, zan batar da su bakidayansu face bayinka katangaggu daga cikinsu.
Nassoshi
- Ibn Tawoos, Ali Ibn Musa, Al-Mujtana Min Al-Dua Al-Mujtaba, ƙum, Dar al-Zhakhar, bugun farko, 1411H.
- Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, Beirut, Darul Fakr, 1407H.
- Ibn Kathir, ƙasas Al-Anbiya wa Akhbar Al-Madin (Kuhlasatu Tarikh Ibn Kathir), bugun Muhammad Ibn Ahmad Kanaan, Beirut, Mu’assasa Al Ma’arif, bugun farko, 1416 Hijira/1996 miladiyya.
- Balaghi, Sadr al-Din, ƙasas ƙur'an, Tehran, Amir Kabir, bugu na 17, 1380H.
- Jazayeri, Nematullah, Al-Nur Al-Mubin fi ƙasas Al-Anbiya wa Al-Mursalin, Beirut, Darul-Azwa, bugu na biyu, 1423H.ttp://vista.ir/article/351963) Labarin Annabi Yusuf (A.S) yana daya daga cikin shahararrun labarai a cikin Alkur'ani mai tsarki da Littafi Mai Tsarki. Wannan labari yana bayyana yadda Annabi Yusuf (A.S) ya fuskanci gwaje-gwaje da jarabawa, daga sayar da shi a matsayin bawa zuwa zama mai mulki a Misra. Labarin yana kuma bayyana yadda Yusuf ya fassara mafarkin Sarkin Misra da yadda ya ceci al'umma daga fari na shekaru bakwai.
- حافظ شیرازی، شمسالدین محمد، غزلیات حافظ، غزل ۲۵۵، وبگاه گنجور، تاریخ بازدید ۳۱ شهریور ۱۳۹۸ش.
- Jafari, Yaƙub, "Namahaye Payambaran dar ƙur'an, Mujallar Makarantar Islama, shekara ta 46, lamba ta 12, Maris 2005.
- Sobhani, Jafar, Manshur Javid, ƙum, Cibiyar Imam Sadik (AS), 1433H.
- Sheikh Sadouƙ, Mohammad Bin Ali, Amali, Tehran, Kitabchi, 1376.
- Sadeghi Tehrani, Mohammad, Al-Furƙan fi Tafsirin al-ƙur'an in the ƙur'an and Sunnah, ƙum, Farhang Shi'i Publications, 1365.
- Safi, Sayyid Muhammad, ƙissahaye ƙur'ani, ƙum, Ahlul Baiti, bugu na biyu, 1379.
- Ziaabadi, Mohammad, Tafsir Surah Yusuf, Tehran, Al-Zahra Charity Foundation (Aliha Salam), 1388.
- Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan a cikin Tafsir Kur'ani, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyar, 1417H.
- Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Al-Wafi, Library of Imam Amirul Momineen (AS), Isfahan, 1406H.
- ƙutbuddin Ravandi, Saeed bin Hebatullah, ƙasase Al-Anbiya Al-Hawi li Ahadisin Kitab Al-Nubuwah, Sheikh al-Saduƙ, ƙum, Allameh Majlesi Publications, 1388.
- ƙommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirul ƙummi, Kum, Darul Kitab, 1404H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-kafi, Tehran, Dar Al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
- Majlesi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar Ledurar Akhbar Al-A'Imma Al-Athar (AS), Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Masoudi, Ali bin Hossein, Isbatul Al-wasiyya Imam Ali bin Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), ƙum, Ismaili, bugu na uku, 2004.
- Ma'arif wa Digaran, "Barasi Riwayat Tafsiri Fariƙaini dar mas'laeh Izdiwaji Hazrat Yusuf ba Zulaikha", mujallu biyu na binciken hadisi = shekara ta 7, lamba ta 13, bazara da rani 2014.
- Maƙdisi, Motaher bin Taher,Al-Mabda'u wa al-Tarikh, Bor Saeed, Islamic Culture School, Bita.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
- Yaƙut Hamavi, Mojam Al-Buldan, wanda aka buga a Beirut, bugu na 2, 1995.